Wasu karin mutane 80 kuma sun sa samu raunuka, kuma an garzaya da su asibiti
Wasu hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna mahajjatan da ke kwance jina-jina, kana ga wasu sassan injin daga kayan da ya fado ta cikin rufin silin.
Injin din ya fado ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara.
Lamarin ya faru 'yan makonni kafin gudanar da Arafa a yayinda maniyyata daga kasashe daban-daban na duniya suka hallara a kasar domin sauke farali.
A bara ne kasar ra Saudia ta kayyade yawan adadin mahajjatan saboda ayyukan gine-ginen a babban Masallacin na Ka'aba.289